RAHOTO: Muna Alfahari Da Nasarar Sojojinmu Kan Boko Haram —Buhari
Daga Sulaiman Bala Idris
A halin da ake ciki dai sojojin Nijeriya, karkashin Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai sun cika alkawarin da suka dauka na kawo karshen rikicin Boko Haram, musamman a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan. Wanda kuma ya jawo wa sojojin fatan alhairi daga sassa daban-daban, tare da jinjina wa gwamnatin Muhammadu Buhari kan wannan namijin kokari.
A yayin da ya ke yaba ma sojojin Nijeriya kan wannan nasarar da suka samu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya babbayana cewa ya yi matukar murna, tare da alfahari da sojojin Nijeriya, a bisa nasarar da suka samu na tarwatsa Boko Haram, tare da kwato hatsabibin dajin nan na Sambisa, wanda a baya ya kasance matattarar ‘yan ta’addan.
A jawabin nasa, Shugaba Buhari ya jaddada cewa za a ci gaba da zage damtse wurin ganin an ‘yanto ‘yan matan Sakandaren nan na garin Chibok, wadanda suka kwashe shekaru a hannun ‘yan Boko Haram din.
Ya kara da cewa, “ina so in yi amfani da wannan dama wurin yaba wa kwazo da jajircewar sojojin nan namu na ‘Operation Lafiya Dole’, wadanda suka tarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram da ake kira da ‘Camp Zero’ da ke cikin dajin Sambisa.
“Shugaban rundunar sojojin kasa, ya sanar da ni cewa an rusa wannan sansanin ne da misalin karfe 1:35 na ranar Juma’a 22 ga watan Disambar 2016, wanda ya sa dole ‘yan ta’addan suka arce, sakamakon tarwatsa mafakar tasu,” in ji Shugaba Buhari.
Daga nan sai Shugaban ya yi kira ga rundunar sojojin Nijeriyar da su ci gaba da fatattakar wadannan ‘yan ta’addan har a wuraren da suke boye, domin a gabatar hukunci a kansu.
Haka kuma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga rundunar sojojin. Ya kuma bukaci jama’a da su taimaka wa sojojin wurin fallasa asiran ‘yan ta’addan da dukkan wata mafaka da suke da ita.
Haka nan su ma Gwamnonin jihohi da wasu jiga-jigai a Nijeriya sun jinjina wa gwamnatin tarayya da sojojin Nijeriya bisa wannan namijin kokari da suka yi a kan lamarin. A wata sanarwa da babban mai ba Shugaban kasa shawara kan kafafen watsa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya samu kiraye-kirayen wayoyi daga Gwamnonin jihohin Jigawa, Kano, Yobe, Adamawa, Borno, Katsina, Kaduna, Sakkwato da wasu Gwamnonin Kudancin Nijeriya, suna nuna jin dadinsu da taya gwamnati murna kan nasarar da aka samu.
Mai taimaka wa Shugaban kasan ya ce, “wannan nasarar ta faranta wa ‘yan Nijeriya rai, shi ya sa ake ta murna a ciki da wajen kasar nan. Haka kuma Gwamnonin sun mika sakon jaje ga sojojin da sua rasa ransu, da sauran al’ummar da suka taimaka wurin ‘yanto dajin Sambisa daga hannun ‘yan boko haram, tare da fatan ba za a manta da sadaukarwarsu ba.”
A wani mataki tamkar na mayar da martani, Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya bayyana a faifen bidiyo a ranar Lahadi 25 ga watan Disambar 2016, yana mai karyata rahotannin tarwatsa su da aka ce yi.
Ya ce, “muna nan kalau, muna nan lafiya, babu inda aka kore mu, kuma dabara ba zai sa a gane inda muke ba, sai in Allah ya so. Mu da Allah muke aiki. Ku daina yi wa mutane karairayi. Idan da gaske ne an tarwatsa mu, ya za a yi kuma in bayyana? Gani nan! Sojojinku suna so su huta ne, shi ya sa suke so su ce sun gama aiki. Karya suke yi, sai nan gaba ma za mu fara. Mu ne Jama’atu Ahlussunati lid da’awati wal jihad, mu ne wanda muna da’awa muna jihadi, muna da Daular kanmu, ba ma cikin Nijeriya.”
Sai dai rundunar Sojojin ta fitar da wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakinta, Birgediya Janar SK Usman, wanda a ciki ta kira faifen bidiyon na Shekau a matsayin wata farfaganda mara amfani. Yana mai cewa ‘yan ta’addan sun shiga matsi ne shi ya sa suka saki bidiyon farfagandar domin su ci gaba da tsoratar da ‘yan Nijeriya. Saboda haka sai rundunar sojojin ta bukaci jama’a da su ci gaba da sa ido a mu’amalolinsu na yau da kullum.
« Previous Article
RAHOTO: Rasuwar Babban Limamin Masallacin Mando Ta Girgiza Jama’a
Comments
Post a Comment